2023: Ganduje ya gargadi yan Siyasa kan yawo da makamai

Date:

Daga Rumaisa Lawan

Gwamnan Jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya ja kunne Yan Siyasa a Jihar nan da su guji Amfani da makamai a wuraren tarukan Siyasa.

Kadaura24 ta rawaito Gwamnan ya bayyana hakan ne yayi da ya jagoranci Kaddamar da Sabbin zababbun Shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Kano ta arewa Wanda ya gudana a Karamar Hukumar Bichi .
Gwamna Ganduje yace Amfani da makamai a wuraren tarukan Siyasa Bai dace da ga yan Siyasa masu manufa ba, Waɗanda kamata yayi su mai da hankali wajen inganta Rayuwar al’ummar su ba lalata Rayuwar Matasa ba.
Yace Jam’iyyar APC a Kano bata da burin da ya wuce inganta Rayuwar al’umma Musamman Mata da matasa domin su ne kashin bayan cigaban kowacce irin al’umma.
Gwamna Ganduje ya Kuma bukaci sabbin Shugabannin jam’iyyar dasu Mai da hankali wajen shiga lungu da sako na yankinsu don su wayar musu da Kai, su fahimci aiyukan alkhairi da jam’iyyar ta Gudanar tsahon Shekaru 8 da suka gabata a Kasar nan.
Wakilinmu ya rawaito mana cewa taron ya sami halartar ‘ya’yan jam’iyyar daga Kananan Hukumomi goma Sha uku dake yankin kano ta arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah : Kansilan Lajawa ya raba Naira dubu 500 ga al’ummar mazabarsa

Daga Nura Adam   Kansilan mazabar Lajawa a karamar hukumar Wudil...

Da dumi-dumi: Kotu ta aike da Matashin dake shigar mata a Tiktok da film gidan gyari

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab'i...

Rabon Jakai: Faizu Alfindiki ya aikawa Sanusi Bature budaddiyar wasika

Zuwa ga: DG. Sunusi Bature Dawakin Tofa Daraktan Yada Labarai, Gwamnatin...

Dama ba mu yi shirin yin hawan babbar Sallah ba – Sarki Aminu Ado Bayero ya fadi dalili

Daga Isa Ahmad Getso   Sarkin Kano na 15 Aminu Ado...