Daga Kamal Yahaya Zakariyya
Hukumar kula da harkokin kasuwanci ta Kamfanin Kingston Organic Plc da ke Landan ta nada kwararre a harkokin hulda da Jama’a Sunusi Bature a matsayin mataimakin shugaban Kamfanin Wanda zai rika kula da ayyukan Kamfanin a Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Califonia, ta kasar Amurka ta hannun wanda ya kafa kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Mista Maurice Frosch.
Mista Frosch ya ce nadin Sunusi Bature a matsayin shugaban ofishin hadin gwiwa na Afirka ta Yamma a matsayin mataimakin shugaban Kamfanin a kasar nan ya fara aiki daga ranar Talata 1 ga Maris, 2022.
Ya ce Sunusi Bature zai kasance a Najeriya ne domin gudanar da ayyukan kamfanin da ke da ayyuka a fadin yankin yammacin Afirka kuma zai yi aiki a matsayin mai kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin wani shahararren kamfanin siyar da kayayyaki ta Najeriya Silvex International Limited, RegenFarm UK da kuma Kingston Organic Plc .
Sunusi ƙwararren malami a harkokin hulda da Jama’a PR kuma yana da ruwa da tsaki a fannin sarrafa ayyuka, sadarwa, bunƙasa kasuwanci, dabarun tallace-tallace da aiyukan kamfanoni, kuma yana da ƙwarewar aiki kusan shekaru ashirin a cikin ci gaban ƙasa da ƙasa, kamfanoni masu zaman kansu da kuma Kafafen yada labarai a Najeriya.
A cikin shekaru 18 da suka gabata, ya gudanar da ayyuka daban-daban da shirye-shirye dangane da harkokin noma, shugabanci, ilimin yara da mata, kula da lafiyar mata da yara, ƙarfafawa mata gwiwa, rayuwa da dai Sauransu.
Shi ne wanda ya lashe lambar yabo ta ilimi ta Cambridge kan aikin jarida a shekarar 2008, Bature ya yi aiki a wurare daban-daban a kungiyoyi daban-daban na kasa da kasa da na kasashen biyu kamar Ofishin Harkokin Waje da Kasuwanci na Biritaniya (FCDO), Hukumar Bunkasa Ci Gaba ta Amurka. (USAID), Bill da Melinda Gates Foundation, Save the Children International, Discovery Learning Alliance da Rockefeller Foundation YieldWise Initiative for Food Security in Africa.
Ya rike mukamai da dama da suka hada da General Manager Corporate Services a Dantata Foods and Allied Products Limited (DFAP), Director Stakeholder Engagement at YieldWise Project, Country Program Manager at Girl Rising (ENGAGE) Project ya tallafa wa Gwamnatin Amurka, Mai Gudanar da Ayyukan Jiha na MNCH Campaign Project. na BMGF, Mataimakin Darakta Ayyuka a Discovery Learning Alliance, Jami’in Shirye-shiryen Jiha, Ba da Shawarwari da Ci Gaban yada Labarai da dai Sauransu.
Sanusi ya kammala digirinsa na farko (B.A. Hons.) a Mass Communication a Jami’ar Maiduguri, ya yi Diploma ta kasa a Mass Communication a Kaduna Polytechnic, Sannan yayi babbar diploma HND da dai Sauransu.
Ya kuma samu MSc. a cikin Ayyukan zamantakewa tare da ƙwarewa a Ci gaban Al’umma daga Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, (LAUTECH) Ogbomosho, Jihar Oyo da kuma wani digiri na biyu a Harkokin Jama’a (MPR) daga Jami’ar Bayero dake Kano, Nigeria. Ya yi digiri na biyu akan Gudanar da Ayyuka a Kwalejin Robert Kennedy, Zurich, Switzerland.