Wahalar man fetur ta jefa yan Nigeria Cikin Mawuyacin hali, ya kamata Buhari ya duba-inji kata kungiya

Date:

Abubakar Sa’eed Sulaiman

 

Ƙungiyar matasan Arewacin Najeriya masu amfani da shafukan sadarwar zamani, tace kamata yayi gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo karshen tsadar man fetur da ake cigaba da fuskanta a halin yanzu a ƙasar nan.

Mai magana da yawun ƙungiyar Kwamared Umar Abdullahi Zango ne yayi wannan jawabin yayin zantawarsa da manema labarai a jihar Kano.

“Matuƙar gwamnatin tarayya bata samar da hanyoyin shan fetur ɗin cikin sauƙi ga al’umma ba, to kuwa shakka babu al’umma zasu cigaba da shan man cikin wahala kamar yadda ake fama a yanzu, inji Umar Zango.

Haka zalika ƙungiyar ta ce, bai kamata dilallalan man fetur su rinƙa ɓoye man idan suka siyo ba, domin kuwa yin hakan ba dai-dai ba ne ba, kasancewar mutane suna cikin halin damuwa wajen shan man.

Umar Zango ya kumace, shugaban ƙungiyar matasan Arewacin Najeriya (Arewa Youths Concern Media Forum) ta Ƙasa reshen jihar Kano, Kwamared Abubakar Basiru Jibaga, ya haƙurƙurtar da ƴan ƙasa da su ƙara haƙuri kan matsalar man fetur ɗin da ake cigaba da fuskanta a Najeriya.

Al’umma da dama dai suna ta nuna damuwarsu kan tsadar man da ake cigaba da fuskanta, wanda a wasu jahohi ake siyar da litar man Naira 600, wasu guraren ma sama da haka, yayin da a wasu jahohin ake siyarwa 190, harma 200.

Aƙalla dai an shafe sama da makwanni biyu ana fuskantar matsalar man fetur ɗin, wanda a wani bangaren ake batun cewar, wahalar man ya samo asali ne biyo bayan samun gurɓataccen man fetur a ƙasar da aka samu a ƴan kwanakin nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...