MAAUN ta yiwa Sarkin Musulmi, Gwamnatin Sakkwato ta’aziyyar  Rasuwar Magajin Gari

Date:

Daga Sayyadi Bashir

Hukumar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), da Franco-British International University (FBIU), ta Kaduna, sun mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalai, Majalisar Sarkin Musulmi da Gwamnatin Jihar Sakkwato, bisa rasuwar Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Danbaba.

Kadaura24 ta rawaito Danbaba, wanda ya rike sarautar Magajin Garin Sakkwato, ya rasu ne a ranar Asabar 12 ga watan Fabarairun, 2022 yana da shekaru 50 a gidansa da ke Kaduna sakamakon gajeruwar rashin lafiya.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wanda ya kafa kuma shugaban Jami’ar Maryam American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya Sanyawa hannu Kuma ya aikowa Kadaura24.

A cewar sanarwar, rasuwar Basaraken babban rashi ne ba ga iyalansa da Majalisar Sarkin Musulmi da jihar Sakkwato kadai ba, har ma da kasa baki daya.

“Na yi matukar kaduwa da samun labarin rasuwar Alhaji Hassan Danbaba, Magajin Garin Sakkwato. Allah Ta’ala ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi a Aljannah Firdausi”. inji farfesa Gwarzo

Ya bayyana marigayin a matsayin mai mutunci kuma kamilin mutum wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban daular Sakkwato da ma Nijeriya baki daya.

“A madadin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, Majalisar Sarkin Musulmi, gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato tare da addu’ar Allah madaukakin Sarki ya sanya shi a Aljannah Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure rashinsa.”

Marigayin ya bar mata uku da ‘ya’ya shida, tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Sakkwato.

Allah ya jikansa da Rahama yasa ya huta, amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...