Gwamnatin Jihar Kogi karkashin jagorancin Gwamnan Yahaya Bello ta amince da aiwatar da biyan ma’aikatan Jihar sabon tsarin albashi na naira dubu talatin.
Sakataren gwamnatin Jihar Mrs Folashade Arike-Ayoade, ce ta sanar da haka bayan ganawa da kungiyar kwadago a garin Lokoja.
Daily News24 ta rawaito Mrs Folashade ta kara dacewa tun farko an sami jinkiri ne wajen aiwatar da sabon tsarin albashin sakamakon rashin ganawar da kwamatin da aka kafa kan tsarin albashin bayayi akai-akai, a sabila da annobar korona.
Dayake jawabi mataimakin gwamnan jihar Chief Edward Onoja, yace abun farinciki ne ace gwamnati ta fara biyan ma’aikata mafi kankantar albashi na naira dubu talatin, inda ya yabawa kungiyar kwadago reshen jihar bisa dattakun da ta nuna batareda sun kai ruwa rana ko tafiya yajin aiki ba.
Shima anasa jawabin shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Mr Onuh Edoka,” yace munji dadi abinda gwamna Yahya Bello yayi, dafari har mun sanar zamu shiga yajin aiki, amma yanzu mun dakatar da wannan batu saboda gwamnati tayi abinda ya kamata tayi’’.