Wani matashi Tijjani Abubakar ya yi yunkurin kashe kansa ta hanyar shan fiya-fiya bayan da budurwarsa ta ce ta daina sonshi.
TIME EXPRESS ta ruwaito matashin dan unguwar Gama PRP ya sha fiya fiyar ne ranar Talata da nufin ya kashe kansa don ya huce takaicin abinda budurwar tasa ta yi masa.
Tijjani Abubakar yace ba Rashin kudi ne yasa ya kasa Samun sahibar tasa ba hasalima yace Yana sana’ar ta harkokin waya a Kasuwar waya ta Farm center Amma Kaddamar ta hana shi samunta duk da kudin da ya kashe a Kanta.
Sai dai an ceto rayuwar matashin kafin fiya-fiyar ta kai ga yi masa lahani a jinkinsa.