A zaman kotun na yau Litinin karkashin mai shari’a Usman Na’abba, Abdulmalik Tanko ya ce kokadan ba shi ya kashe Hanifa Abubakar ba kuma bashi da masaniya kan aikata kisan.
Kadaura24 ta rawaito bayan da aka gurfanar da shi a gaban babbar kotun jiha ranar litinin wanda ake zargin ya ce ya yarda ya sace ta amma bashi ya kashe ta ba.
Idan za a iya tunawa dai a baya Abdulmalik Cikin Wani faifen video da Jami’in hulda da Jama’a na yan sandan Jihar Kano ya wallafa a Shafin Facebook, ya amsa kisan Hanifa bayan da rundunar ‘yan sanda ta yi holinsa a shalkwatarsu.
Har ma ya bayyana cewar ya kasheta ne da shinkafar bera ta N100 bayan da ya saceta ya kuma boyeta a wani wuri.
Wannan ce ta sanya alkalin kotun ya dage shari’ar har zuwa ranar 2 da 3 ga Maris mai kamawa domin sauraron karar, ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsareshi a gidan yari.