Daga Zakariyya Adam Jigirya
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci jami’an tsaro da su gaggauta bankado wadanda suka kashe Rukayya Mustapha, matar aure da wasu ‘yan bindiga suka kashe a unguwar Danbare dake nan Kano.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da yake jajantawa iyalan mamaciyar a unguwar Dorayi dake karamar hukumar Kumbotso a jihar.
Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa fagge ya aikowa Kadaura24 yace wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.
” cikin tsananin kaduwa muka samu labarin rasuwar Marigayiya Rukayya Mustapha… Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu bar wani abu haka kawai ba, dole sai an nemo Waɗanda Suka aikata Wannan mummunan aiki”. Inji Ganduje
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar ina Allah wadai da wannan aika-aika tare da addu’ar Allah ya jikan ta yasa tana Jannatul Firdaus tare da baiwa ‘yan uwanta hakurin jure rashin”. Ganduje ya ce”.
A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayyana cewa kawo yanzu an kama mutane 5 da ake zargi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka kashe matar .
Ya kuma yi nuni da cewa, wadanda suka yi ta’ammali da miyagun kwayoyi ne suke aikata irin wadannan laifuffuka, shi ya sa suke kama duk wadanda suke yi safarar miyagun kwayoyi domin dakile sake afkuwar lamarin.
Dikko ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumomin tsaro za su rubanya kokarinsu na ganin ba’a sake Samun Faruwar irin wadannan laifuka ba nan gaba.
Tawagar ta kunshi kwamishinoni, Daraktan DSS Alhassan Muhammed da shugaban karamar hukumar Kumbotso Hassan Garban Kauye.