Daga Rukayya Abdullahi Maida
Majalisar Zattarwa ta kasa ta amince da baiwa mutane dari biyu da tamanin da shida yan kasashen waje takardar izinin zama yan Najeriya.
KADAURA24 ta rawaito Ministan harkokin Gidan Rauf Aregbesola ne ya sanar da haka ga manema labaran Fadar Shugaban Kasa, bayan kammala zaman Majalisar Zartarwar ta Kasa na Wannan makon a Fadan shugaban kasa.
Yace akwai Mutane da dama yan kasashen waje Waɗanda suke sha’awar Zama Yan Nigeria, Kuma Muna binsu Muna tsantsancewa don gudun kada a yi kitso da kwarkwata”.
Ministan yace daga Cikin Waɗanda suka halacci tantancewa da akai Musu domin Zama cikakkun Yan Nigeria sun fito ne daga kasashen Amuruka da Australia da yan kasashen larabawa da dai Sauransu.
” Daga Cikin Waɗanda muka tantance mun Sami Mutane dari biyu da tamanin da shida (286) Waɗanda Suka chanchanci Gwamnati ta basu shaidar Zaman cikakkun Yan Nigeria”. Inji Ministan
Rauf Aregbisola yace Wannan Wani Abu ne da ya kamata ‘yan Nigeria su Maida hankali wajen Gina Kasar, Inda yace Yayin da Wasu daga cikin Mutanen Kasar nan suke komawa Zuwa Wasu kasashen, sai gashi Wasu daga kasashe daban-daban Suna son su zama Yan Nigeria.