Rikicin APC a Kano: Ganduje ya ce ya shirya tsaf domin fara aikin da APC ta dora masa a gobe Juma’a

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
 Shugaban kwamitin hadin gwiwa na jam’iyyar APC na kasa/jiha, kuma gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa kwamitin ya kammala shirye-shiryen karbar sauran mambobin kwamitin domin gudanar da taron sasantawa jihar a gobe.
 Cikin Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya aikowa Kadaura24  ya ruwaito gwamnan na cewa an tanadi wurin da za a gudanar da taron da aka shirya farawa a ranar Juma’a 11 ga watan Fabrairu, 2022 a babban birnin jihar nan.
 Gwamna Ganduje ya tabbatar wa ‘ya’yan sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar cewa a shirye kwamitin ya ke na baiwa Kowa dama da nufin kawo hadin kai da ci gaba a jam’iyyar a jihar kano da kasa baki daya.
 Kwamitin wanda Sakatariyar jam’iyyar ta kasa ta kafa, ya kunshi mambobi kamar Sardaunan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Gwamna Bello Matawalle, Hon. Yakubu Dogara da Sanata Abba Ali.
Uwar jam’iyyar APC ta kasa dai ta baiwa Kwamitin kwanaki bakwai ya kammala aikinsa zai mika rahotonsa.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Bayan Shugaban Kwamitin Rikon APC na Kasa Mai Mala Buni ya sanar da Kafa Kwamitin karkashin Gwamna Ganduje bangaren su Sanata Malam Ibrahim Shekarau sun yi watsi da Matakin na uwar jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...