Daga Rukayya Abdullahi Maida
Yayin da ya rage saura kwanaki biyu a gudanar da zaben sabbin shugabannin shiyyoyi na jam’iyyar PDP, jam’iyyar reshen jihar Kano ta sake tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Sanata Bello Hayatu tun da farko Wanda aka zarge shi da yiwa Jam’iyyar zagon kasa a zaben 2019.
Hakan na kunshe Cikin Wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar kano Alhaji Shehu wada sagagi ya Sanyawa hannu Kuma aka aikowa Kadaura24.
“A yayin da muke tunkarar babban taron jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma, shuwagabannin jam’iyyar PDP na jihar Kano da shugabannin kananan hukumominta 44 sun gana a ranar Laraba 9 ga watan Fabrairun 2023 inda suka amince da dakatar da shi daga jam’iyyar saboda alakarsa da jam’iyyar APC da kuma yiwa PDP zagon Kasa kamar yadda aka zarge shi tun daga mazabarsa lokacin babban zaben 2019”. Inji sanarwar Sagagi
Idan zaku iya tunawa mazabar Gwarzo ta fitar da sanarwar dakatar ga Sanata Bello Hayatu Gwarzo kuma Kwamitin zartarwa na kananan hukumomi da na jiha suka amince da dakatarwar.
“Muna fata kwamitin koli na kasa da kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP cewa muka bi tsarin da ya dace kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ta PDP ya tanada, Wanda dakatar da Sanata Gwarzo Kamar yadda aka bi wajen dakatar da tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Prince Uche Secondus kuma a yau, NWC mai ci a yanzu ita ce ta fi cin gajiyar irin wannan tsari bisa ka’ida ta tsarin mulkin jam’iyyarmu”. Inji Sagagi
“Ina so in tabbatar da cewa a yau na samu umarnin kotu na umurtar Shugabannin jam’iyyar mu ta kasa da ta jaha da su dakatar da Sanata Bello Hayatu daga shiga zaben shiyyar Arewa maso Yamma mai zuwa”.
Sanarwar tace ya zama dole su a matsayinsu na jam’iyya su yi biyayya ga umarni kotu don guje wa matsalar da Rashin bin Umarnin Zai haifarwar jam’iyyar a babban zaben 2023 mai zuwa.
A bayyane yake, Sanata Bello Hayatu ya yi aiki don Gwamna Ganduje ya Sami nasara a 2019 kuma Gandujen ya sallame sh ta hanyar nada makusancinsa a matsayin Manajan Darakta na gidan zoo na Kano da wasu masu ba da shawara na musamman a gwamnatin Ganduje.
Sanarwar ta Kara da Cewa Don haka kwamitin zartarwa na jihar ya sake tabbatar da dakatar da Sanata Gwarzo, saboda haka ba shi da hurumin tsayawa takara a jam’iyyar.