Gidauniyar Kashe kwabo dake Gwale ta yiwa yara 50 kaciya

Date:

Daga Ibrahim Abubakar Diso
Gidauniyar umar kashe kwabo dake Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano ta yiwa yara hamsin kaciya tare da basu magani kyauta.
 an dai gudanar da wannan aiki ne a asibitin sha ka tafi dake Gwale kusa da ofishin hisba karkashin kulawar Sagir Ibrahim.
Shugaban gidauniyar Alh. Umar kashe kwabo yace yana daga cikin aikin wannan gidauniya tallafawa marasa karfi don ganin an fitar dasu daga cikin wani kangi.
Ya Kuma kara da cewa ko a ranar asabar din da ta gabata gidauniyar ta rabawa dalibai litattafai a unguwar Gwale tare da basu uniform kyauta, yace fatansu Allah ya fisu yaba wannan aiki da suke yi.
 Wasu da cikin iyayen yaran da akaiwa kaciyar sun godewa shugaban gidauniyar tare da  ina yin addu’ar o’ Allah ya dada bunkasa wannan gidauniya ta cigaba da tallawa marasa karfi.
Malam Sagir wanda yayi matukar nuna farin cikinsa dangane da kokarin da wannan gidauniya take yi, sannan ya ja hankalin masu hannu da shuni da suyi koyi da wannan gidauniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...