Za mu mika Abba Kyari ga Amurka idan suka bukaci hakan – Abubakar Malami

Date:

Hukumomi a Najeriya na iya mika wa Amurka jami’in dan sanda Abba kyari domin ya fuskanci tuhume-tuhumen da hukumar ‘yan sandan Amurka ta FBI ke yi masa idan bukatar haka ta taso.

Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da yayi da tashar talabijin ta Channels.

Ministan ya ce hukumomin Najeriya na aiki tare da jami’an Amurka kan tuhume-tuhumen da ake wa Abba Kyari da mutumin da ake tuhuma da aikata damfara ta intanet wato Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi: “Wannan batu ne da ya shafi yin aiki tare tsakanin kasa da kasa kuma muna aiki tare, kana ana samun ci gaba.”

Sai dai Minista Malami bai ce komai ba kan abin da gwamnatin Najeriya za ta yi idan Amurka ta bukaci a mika ma ta Abba Kyari in ban da cewa kawo yanzu kasashe na ci gaba da duba batun.

“Akwai batutuwa masu yawa da muke dubawa tare, ciki har da yiwuwar mika Abba Kyari, saboda haka ne hadin kai kan batun ke da muhimmanci matuka kan wadannan batutuwan.”

‘Yan sandan Najeriya sun fara binciken tuhume-tuhumen da ake wa Abba kyari ne bayan da wasu bayanai suka fito daga hukumar ‘yan sanda ta FBI kan alakarsa da dan damfara Hushpuppi wanda a halin yanzu ke tsare a wani kurkukun Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...