Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Wata Kotu a Jihar Kano ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a gidan hali ba tare da zabin tara ba ga jarumar Kannywood, Sadiya Haruna.
Mai Shari’a Mukhtar Dandago na kotun dake filin jirgin sama na malam Aminu Kano ya ce kotun dai ta Kama Sadiya Haruna da Laifin bata sunan jarumin Kannywood Isa A Isa.
Sadiya Haruna dai ta yi kalaman ne a cikin wani faifan bidiyo data wallafa a shafinta na Instegram, Inda ta zargi dan wasan ya bukaci ya yi mata lalata da ita.