Uwar jam’iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa ba ta rantsar da shugabannin jam’iyyar na kano ba

Date:

Daga Halima M Abubakar

Uwar Jam’iyar APC ta Ƙasa ta bayyana dalilin da ya sanya ba ta rantsar da shugabannin jam’iyar na Jihar Kano ba.

Kadaura24 ta rawaito cewa a ranar Alhamis da ta gabata ne dai jam’iyar ta rantsar da shugabannin jam’iya na jiha a jihohi 34 amma banda Kano da Sokoto.

Da ya ke bayani a kan dalilan da ya sanya ba a rantsar da shugabannin jam’iya na Kano ba a jiya Juma’a a Abuja, Sakataren Kwamitin Riƙo na APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe, ya ce babu wani abin damuwa a kan matakin.

A cewar sa, uwar jam’iyar ta ɗauki matakin dakatar da rantsar da shugabannin jam’iya na Kano ne domin amfanin ƴan jam’iyar, jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ya ce APC na son zaman lafiya kuma Kano ta zama kamar nan ne Shalkwatar jam’iyar, inda ya ce ba za a yi wani abu da zai kawo naƙasu ga zaman lafiyar jam’iyar a jihar ba.

Daily Nigerian ta rawaito Akpanudoedehe ya ƙara da cewa akwai maganar shari’ar jam’iyar a kotu, sabo da haka uwar jam’iyar taki yin abun da zai zama kuskure a gareta ba Saboda lamarin na gaban kotu.

Sai dai kuma Akpanudoedehe bai fadi dalilin da ya sa jam’iyar ba ta rantsar da shugabannin jam’iya na Sokoto ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...