A jiya Juma’a ne dai kwamitin sulhun rikicin jam’iyar APC a Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC na Ƙasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sake zaman sulhunta tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Kadaura24 ta rawaito cewa a zaman da a ka yi na ranar Talatar da ta gabata, Ganduje bai halarta ba bai kuma tura wakili ba hakan tasa aka dage Zaman zuwa ranar Juma’ar.
Majiyoyi sun ce gwamnan bai halartar zaman ba ne sabo da ya na da yaƙinin samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara, bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɗan takarar sa na shugabancin jam’iya na jiha, Abdullahi Abbas.
sai dai gwamnan ya samu halartar zaman na jiya Juma’a bayan da a ranar Alhamis, kwamitin riƙo na jam’iyar ya rantsar da shugabannin jam’iya na jiha na jihohi 34, amma ban da Kano da Sokoto.
A zaman sulhun dai na jiya, wanda a ka kwashe kusan awanni shida a na tattaunawa, ba a cimma matsaya ba.
Sai dai kuma kowanne ɓangare ya miƙa kundin buƙatarsa ta yadda ya kamata a kasafta muƙaman jam’iya ga shugaban kwamitin, Buni.
Kwamitin kuma zai yi nazari a kan buƙatun da kuma kasafta muƙaman, inda da ga bisani za a sake kiran zaman a shaidawa ɓangarori biyun irin kasafin muƙaman da kwamitin ya yi.
Amma wasu majiyoyi da su ke cikin zaman sulhun sun shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa zai yi wuya duka ɓangarori biyun su amince da kasafin.