Rikicin APC a Kano: Ganduje da Shekarau sun miƙa buƙatun su na kasafta muƙaman Jam’iyya ga kwamitin sulhu

Date:

 

A jiya Juma’a ne dai kwamitin sulhun rikicin jam’iyar APC a Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riƙon Ƙwarya na APC na Ƙasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sake zaman sulhunta tsakanin ɓangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Kadaura24 ta rawaito cewa a zaman da a ka yi na ranar Talatar da ta gabata, Ganduje bai halarta ba bai kuma tura wakili ba hakan tasa aka dage Zaman zuwa ranar Juma’ar.

Majiyoyi sun ce gwamnan bai halartar zaman ba ne sabo da ya na da yaƙinin samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara, bayan da wata Babbar Kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɗan takarar sa na shugabancin jam’iya na jiha, Abdullahi Abbas.

sai dai gwamnan ya samu halartar zaman na jiya Juma’a bayan da a ranar Alhamis, kwamitin riƙo na jam’iyar ya rantsar da shugabannin jam’iya na jiha na jihohi 34, amma ban da Kano da Sokoto.

A zaman sulhun dai na jiya, wanda a ka kwashe kusan awanni shida a na tattaunawa, ba a cimma matsaya ba.

Sai dai kuma kowanne ɓangare ya miƙa kundin buƙatarsa ta yadda ya kamata a kasafta muƙaman jam’iya ga shugaban kwamitin, Buni.

Kwamitin kuma zai yi nazari a kan buƙatun da kuma kasafta muƙaman, inda da ga bisani za a sake kiran zaman a shaidawa ɓangarori biyun irin kasafin muƙaman da kwamitin ya yi.

Amma wasu majiyoyi da su ke cikin zaman sulhun sun shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa zai yi wuya duka ɓangarori biyun su amince da kasafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...