Kotu ta bayar da belin Muaz Magaji Dan Sarauniya bisa wasu sharudda

Date:

Wata kotu a Jihar Kano da ta bayar da belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Mu’azu Magaji Dan Sarauniya.

Kotun mai lamba 58 da ke zamanta a unguwar Nomansland ta bayar da belin ne kan naira miliyan daya, tare da gindaya masa wasu sharuda da sai ya cika belin zai bayu.

BBC Hausa ta rawaito mai shari’a Aminu Gabari ya ce bayan biyan kudin da Dan Sarauniya zai yi sai ya kuma ajiye fasfo dinsa na tafiya.

Kazalika zai kawo mutum biyu da za su tsaya masa, dole na farko ya zama mai garin kauyen Sarauniya wato kauyen da ya fito, na biyun kuma dole ya zama limamin garinsu ko kuma kwamandan Hizban garin.

A ranar 27 ga watan Janairun da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama Injiniya Mu’azu a Abuja babban birnin Najeriya.

An kuma mayar da shi jihar Kano inda ‘yan sanda suka gabatar masa da tuhume-tuhumen da ake zarginsa da su, na keta mutunci gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...