Gobara ta kone mai gida, uwar gida da dan su a unguwar kadawa dake kano

Date:

Daga Ussaini Minjibir

 

Wutar lantarki mai ƙarfi ta haddasa gobarar da tayi sanadiyyar mutuwar maigida da matarsa da ɗansu mai shakara uku a aduniya.

Kadaura24 ta rawaito gobarar ta tashi da misalin karfe goma sha biyu na daren alhamis din data gabata a unguwar Maƙera dake kadawa miltara, inda ta ƙone mata da miji da kuma ɗansu mai shakara uku a aduniya.

ƙanin maigidan mai suna Umar Yahaya ya shaidawa Kadaura24 cewa  Marigayin mai suna Anwar Yahaya ƙaninsa ne mai kimanin shekaru talatin da biyu ita kuma matar mai suna Fatima Idiris tana ma ɗauke da juna biyu Allah ya karɓi rayuwar su.

Sakon taya Murnar Samun shugabancin jam’iyyar SDP a Jihar Kano.

 

Ya kuma ce gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki mai ƙarfi da aka kawo a unguwar tasu kuma yayi ƙoƙarin fitowa daga ɗakin amma ya al’amarin ya gagara.

Sai da safe ne makwabta suka haura suka tarar tuni rai yai halinsa.

An kuma yi musu sallah kamar yanda addini ya tanadar, Inda aka kai su maƙabartar unguwar miltara  .

shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano comrade Sale Aliyu jili ya kai musu ziyarar ta’aziyya Inda lamarin ya afku, tare kuma da basu kayan tallafi da suka haɗa da katifu da kwanan rufi da shinkafa da masara da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...

Kananan Hukumomin Tarauni Rogo da Doguwa sun zamo koma baya wajen yin rijistar Masu zabe a Kano

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu kananan hukumomin...

Taron Zuba Jari na Bauchi: Sabuwar Damar Bunƙasar Tattalin Arziki – Daga Lawal Muazu Bauchi

  Ga dukkan alamu, Jihar Bauchi na fitowa a hankali...