Daga Halima M Sadeeq
Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta shigar da karar Shugaba Buhari gaban kotu “kan gaza gudanar da bincike game da zargin da ake yi na batan kudaden da suka kai naira biliyan 3 daga ma’aikatar kuɗi ta kasar, domin tabbatar da an gurfanar da wadanda ake zargi da hannu ciki da kuma kwato kudaden.”
Karar ta biyo bayan batan dabon da ake zargin da ofishin babban akanta janar na kasar ya shigar a 2018 da 2019 na rahoton da yake fitarwa, wanda aka batar da su ba bisa ka’ida ba ko kuma ba a bayar da bayanansu ba.

BBC Hausa ta rawaito karar mai lamba FHC/L/CS/148/22 an shigar da ita ne a ranar Juma’ar da ta gabata a wata babbar kotun Tarayya da ke Lagos, kamar yadda SERAP ta bukata:
“umarnin da zai sanya Shugaba Buhari ya tabbatar da an gudanar da bincike game da zargin da ake yi na batan naira biliyan 3.1 wadanda kudaden mutanen Najeriya ne, a gabatar da duk wanda ake zargi gaban kotu, kuma a kwato kudaden al’umma.”