Daga Adam Bichi
Wani mummunan hadarin mota ya afku a kan titin Aminu Kano, da ke unguwar Goron Dutse, yayin da wani Driban mota kirar Toyota Corolla ke yunkurin wuce wata motar kirar Peugeout 406.
KADAURA24 ta rawaito waddanda suka gane wa idonsu yadda hadarin ya afku, sun ce hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce-sa’a da direban Corollar yake yi.
Afkuwar hadarin ke da wuya, sai tawagar Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ta iso wurin. Nan take Kwamishinan, wanda yake kuma kwararren likita ne, ya nuna tausayawarsa, ya ba da gudumawar gaggawa, kuma ya umarci a dauki wadanda suka ji rauni kafin a kai su zuwa asibiti.

Cikin Sanarwar da jami’in hurda da jama’a na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano Sunusi A. K/Naisa ya aikowa Kadaura24 yace, Dakta Getso ya yi addu’ar samun sauki ga wandanda suka ji raunuka. Sannan ya gargadi direbobi da su guji tukin ganganci da gudun-wuce-sa’a.
Kwamishina Dakta Getso ya ba da gudunmawar ne lokacin da yake kewayen duba aikin tsaftar Muhalli na karshen wata. Yayin zagayen, Dakta Getso yana tare da kwamitin kar ta kwana na Tsaftar Muhalli na jiha wanda ya kunshi jami’an Ma’aikatar Muhalli da jami’an tsaro da ‘yan jarida.