Hadarin Mota: Kwamishinan muhalli na Kano ya kai daukin gaggawa, ya ceci Waɗanda suka jikkata

Date:

Daga Adam Bichi

Wani mummunan hadarin mota ya afku a kan titin Aminu Kano, da ke unguwar Goron Dutse, yayin da wani Driban mota kirar Toyota Corolla ke yunkurin wuce wata motar kirar Peugeout 406.

KADAURA24 ta rawaito waddanda suka gane wa idonsu yadda hadarin ya afku, sun ce hadarin ya faru ne sakamakon gudun wuce-sa’a da direban Corollar yake yi.

Afkuwar hadarin ke da wuya, sai tawagar Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ta iso wurin. Nan take Kwamishinan, wanda yake kuma kwararren likita ne, ya nuna tausayawarsa, ya ba da gudumawar gaggawa, kuma ya umarci a dauki wadanda suka ji rauni kafin a kai su zuwa asibiti.

Sakon taya Murnar Samun shugabancin jam’iyyar SDP a Jihar Kano

Cikin Sanarwar da jami’in hurda da jama’a na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano  Sunusi A. K/Naisa ya aikowa Kadaura24 yace, Dakta Getso ya yi addu’ar samun sauki ga wandanda suka ji raunuka. Sannan ya gargadi direbobi da su guji tukin ganganci da gudun-wuce-sa’a.

Kwamishina Dakta Getso ya ba da gudunmawar ne lokacin da yake kewayen duba aikin tsaftar Muhalli na karshen wata. Yayin zagayen, Dakta Getso yana tare da kwamitin kar ta kwana na Tsaftar Muhalli na jiha wanda ya kunshi jami’an Ma’aikatar Muhalli da jami’an tsaro da ‘yan jarida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...