Gidauniyar Nafisa Charitable ta horar da mata 100 sana’o’i daban-daban

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Gidauniyar Hajiya Nafisa charitable foundation ta kaddamar da horar da yan mata da zawarawa sana’o’i har Guda 100 domin su dogara dakawunsu.
“An Samar da Shirin ne domin ganin an rage musu radadin halin babu da wasu daga cikin al’umma suke fama dashi a wannna lokaci”.
KADAURA24 ta rawaito da take bayani shugabar gidauniyar Hajiya Nafisa Sulaiman tace Gidauniyar ta Saba gudanar da irin wannan Aiki, kuma wannan shi ne karo na hudu da gidauniyar take horar da matan sana’o’i daban-daban.
Sakon taya Murnar Samun shugabancin jam’iyyar SDP a Jihar Kano
Tace an kwashe kwanaki biyu ana bada horon don su fahimci aikin yadda ya kamata, Inda tace tana fatan Waɗanda suka ci gajiyar shirin zasu yi  Amfani da damar ta hanyar data dace.
Maryam Aliyu da Nusaiba Sani na daga cikin Waɗanda aka koyawa sana’o’in sun Kuma bayyana farin cikinsu tare mika godiyarsu ga Hajiya Nafisa Foundation.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...