Daga Sayyadi Abubakar
Uwar jam’iyyar SDP ta kasa ta amince da rushe shugabancin jam’iyyar na kano tare da kafa kwamitin rikon kwarya domin tafiyar da harkokin jam’iyyar a nan kano.
KADAURA24 ta rawaito Cikin wata wasika mai kwanan watan 14 ga watan wannan wata na janairu wasu jagororin jam’iyyar ta SDP a kano sun roki uwar jam’iyyar data rushe shugabancin jam’iyyar saboda wasu dalilai na rashen tafiyar da harkokin jam’iyyar yadda ya dace a jihar kano.
Wasikar koken mai dauke da sa hannun sakataren kwamitin tuntuba na jam’iyyar na kasa Yusuf Buhari da mambobin kwamitin na tuntuba Muhammad Bakin zuwa da Nastura ashir Sharif sun ce shugabancin baya gudanar da aikin kamar yadda aka dora masa kuma sun gaza ciyar da jam’iyyar gaba dai ma koma baya suke haifarwa jam’iyyar ta SDP a nan kano.
Tuni dai uwar jam’iyyar ta SDP ta kasa ta amince da rushe shugabannin jam’iyyar a kano tare da maye gurbinsu da kwamitin riko wanda ake sa rai zai tafiyar da harkokin jam’iyyar har na tsahon kwanaki 90.
Hon. Ali Shattima shi aka nada a Matsayin Shugaban Kwamitin rikon jam’iyyar a kano
Hon. Ali Shatima shugaba
Hon. Hussaini Mai Riga Sakatare
Alh. Sani Mahmud Vice central
Mallam Sale Matugwy Vice Chairman- South
Amb. Munir Sarki Adamu:
Sakataren tsare-tsare
Alh. Zangina Ahmed: Sakataren Yada Labarai
Alh. Abubakar Ibrahim Mukamin S Ma’aji
Barr. Nadia Ado sakatariyar harkokin shari’a
Alh. Abubakar Ali Ado Shugaban matasa
Hajiya Ummi Kabir shugabar mata
Rilwan Muhammed Gurduba: jami’in walwala
Alh. Yusuf Ali Shanono: mataimakin sakatare
Alh. Dahiru Abdullahi: mataimakin ma’aji
Alhaji. Yunusa Abdulkarim: mataimakin jami’in walwala
Cikin wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar SDP na kasa Alhaji Shehu Musa Gabam (Makaman Tilde) ya bukaci sabbin shugabannin jam’iyyar ta SDP a kano dasu hada kan yan jam’iyyar domin samun nasarar zabe mai zuwa na shekara ta 2023.
An intriguing discussion is worth comment. I believe that you should publish more about this issue, it may not be a taboo subject but generally people don’t speak
about these topics. To the next! Best wishes!!