Daga Maryam Muhd Zawaciki
An kaddamar da littafin tarihin garin zawaciki dake karamar hukumar kumbotso a jihar kano wanda Abubakar Yahuza Yakubu Zawaciki ya rubuta.
Da yake bayyana makasudin rubuta littafin Abubakar yahuza yakubu yace ya wallafa littafin ne saboda yadda garin yake da dadadden tarihi amma kuma babu tarihinta a rubuce.
Abubakar Yahuza yace akwai yara masu tasowa da suke bukatar sanin tarihin garin duba da yadda garin yake kara habbaka tare da samun cigaba a kowanne lokaci.
Marubucin littafin yace ya fuskanci kalubale mai yawa yayin da yake kokarin rubuta littafin, Inda yace ya sami shekaru uku yana rubuta littafin, amma dai yace babbar nasarar da ya samu ita ce kammala littafin.
Yayin da yake nasa jawabin mai garin zawaciki mallam Abdulkhadir mu’azam zawaciki ya nuna matukar farin cikin sa dangane da samar da littafin tarihin garin na zawaciki.
Mai garin yace wannan abin Alfahari ne ka san,cewa garin yana da kyakyawan tarihi kuma a kasamu matashi dan gwagwarmaya ya shiga ya fita har ya samar da tarihin garin zawaciki domin Jama’ar garin.
Mai garin yayi Kira ga matasa da suyi koyi da wannan matashin mai shekara 34 wajen ganin suma suna bawa al’umma gudumawar da tadace.
Shima a nasa jawabin Farfesa Muhammad Bello Shitu ya nuna farin cikin sa ga Abubakar matashi Dan gwagwarmaya da yayi tunanin bijiro da tarihin kuma bar ya wallafa tarihin garinnasa.
Farfesa Shitu ya kara da cewa suna da kugiyoyi da suke bawa matasa kwarin gwaiwa wanda Abubakar yahuza yana daya daga cikin matasan da suka tallafawa wajen ganin ya rubuta litafin tarihin garin zawaciki.