2023: Bayan Rikicin APC a Gombe, Jam’iyyar ta Sulhunta Danjuma Goje da Gwamna Yahaya Inuwa

Date:

Daga Abdulrasheed B Imam

 

Kwamitin Rikon Jam’iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya sulhunta tsakanin Gwamna Muhammad Yahaya Inuwa na Jihar Gombe da kuma abokin burmin sa na siyasa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Ɗanjuma Goje.

Jami’in Yaɗa Labarai na Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar, Mamman Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar data gabata a Abuja.

Sanarwar ta ce Buni, da Shugaban Kwamitin Sulhu na APC, Sanata Abdullahi Adamu da tsohon Gwamnan Jihar Borno Kashim Shattima, mamba a kwamitin, su ne su ka jagoranci sulhun.

Sanarwar ta ce wannan shi ne karon farko da manyan ƴan siyasar na Gombe su ka haɗu tun bayan da rigimar siyasa ta ɓarke tsakanin su a shekarar bara.

Mai Mala Buni, Matsayin sa na Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar APC ta kasa ya baiyana jin daɗin sa game da sulhun da a ka yi.

Ya kuma yi alwashin sulhunta duk masu ruwa da tsaki a APC domin ƙarfafa jam’iyar yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...

KANFEST 2025: Gwamna Abba ya umarci sarakunan Kano da su ci gaba da hawan sallah

  Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci...

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...