Wani Yaro Dan Shekaru 4 Rasu Bayan ya fada Rijiya a Kano

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai shekaru hudu Mai Suna Mustapha Dalhatu a Kofar Dawanau dake karamar hukumar Ungoggo a jihar.
 Jami’in hulda da jama’a na hukumar SFS Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a kano.
 Ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran ceto daga wani Aminu Sani Shu’aibu cewa wani karamin yaro ya fada cikin rijiya.
 Saminu Yusif ya yi nuni da cewa, da tawagar su ta isa ta yi nasarar ceto yaron Cikin Mawuyacin Halin, inda daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsa.
 Ya ce an mika gawar marigayin ga hakimin unguwar Dawanau, Alhaji Musa Habibu.
 Hakazalika, ‘yan kwana-kwana na jihar Kano sun kashe wata gobara da ta tashi a layin ‘Yan Robobi da ke Kasuwar Kofar Wambai a karamar hukumar Kano.
 Da yake bayyana lamarin kakakin hukumar ya ci gaba da cewa shago daya gobarar ta shafa.
 Ya ce babu wani rai da aka rasa a lokacin faruwar lamarin, sakamakon daukin gaggawar da hukumar kashe gobara ta Kano ta Kai Wajen.
 Jami’in hulda da jama’a ya bukaci jama’a da su tabbatar da daukar matakan hana Faruwar gobara a kowanni lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...

Kungiyar Karamci United Family ta Karrama Shugaban gidan Radiyon Pyramid Saboda Taimakawa Al’umma

Shugaban gidan Radio tarayya Pyramid FM Dr. Garba Ubale...

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...