Majalisar Koli ta Harkokin Shari’ar Musulci ta Kasa ta Nada Sabon Shugaba

Date:

Daga Aliyah M Sadeeq

Majalisar koli Mai kula da harkokin Shari’ar Musulci ta Kasa, ta nada Mataimakin Shugaban Majalisar na daya Sheikh Abdulrasheed Hadiyatullah a Matsayin Shugaban Majalisar bayan Rasuwar Shugabanta Dr. Ibrahim Datti Ahmad .

Kadaura24 ta rawaito Sakatare janar na Majalisar Nafu’u Baba Ahmad ne ya bayyana hakan Yayin taron Manema labarai a nan Kano.

Sakataren Majalisar yace an nada Shaikh Abdurrashid Hadiyatullah a Matsayin Sabon Shugaban Majalisar ne dogaro da kundin tsarin mulkin Majalisar Wanda ya ce Idan Shugaba ya rasu Mataimakinsa za’a nada domin ya cigaba da tafiyar da harkokin Majalisar.

Gabanin bayyana bayyana Sunan Sabon Shugaban Sai da Majalisar ta Mika ta’aziyyar ta ga iyalai da Yan uwan Dr. Ibrahim Datti Ahmad Wanda Allah ya yiwa Rasuwa makon da ya gabata tare da nema masa rahamar Ubangiji.

Sannna Nafi’u Baba Ahmad ya Yi fatan Allah ya rikawa Sabon Shugaban Majalisar tare da bada tabbacin ‘ya’yan Majalisar zasu bada goyon baya ga Sabon Shugaban Sheikh Abdulrasheed Hadiyatullah.

1 COMMENT

  1. เราคือเว็บดูหนังฟรีออนไลน์ หนังใหม่ชนโรง 2022 เต็มเรื่อง มาให้ท่านได้เลือกชมกันแบบชัดๆ
    หนังมาสเตอร์ MASTER หรือหนังใหม่เสียงซาวด์แทรก ซับไทย บรรยายไทย ก็มีให้เลือกจากตัวเล่น ดูหนังออนไลน์ ของแต่ละเรื่องครบทุกประเภทหนัง
    ได้แก่ ดูหนังแอคชั่น หนังบู๊มันๆ, หนังดราม่า,
    หนังโรแมนติก, หนังสยองขวัญ หนังผี, หนังเกาหลี ดูซีรี่ย์, หนังสืบสวนสอบสวน, หนังซุเปอร์ฮีโร่ MARVEL DC, หนังการ์ตูน แอนิเมชั่น ,
    หนังภาคต่อ หนังดังทั้งไทย
    เอเชีย และต่างประเทศ เป็นต้น

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...