Dangote ya kaddamar da shirin samar da abinci mai gina jiki a Kano

Date:

Daga Hafsat Abdullah
 Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta fara aiwatar da shirinta na samar da abinci mai gina jiki mai taken: Aliko Dangote Foundation Integrated Nutrition (ADFIN) a jihar Kano.
 A cewar Daraktan Lafiya da Abinci na Gidauniyar, Dakta Francis Aminu, yace shirin ya yi dai-dai da shirin yin amfani da sabbin tsarin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da aka gwada a fadin kananan hukumomin 5, Wannan na a matsayin tsarin kula da marasa lafiya da Kuma Masu fama da tamowa.
 A halin da ake ciki, an horar da ma’aikatan lafiya masa da 30 a Kano.
 Dr. Aminu ya ce an gudanar da shirin horon na kwanaki 5 tsakanin 17 zuwa 22 ga Disamba 2021.
 “Makasudin bayar da horon shi ne baiwa ma’aikatan lafiya dabarun da ake bukata kan tantancewa da kula da yara ‘yan kasa da shekaru biyar masu fama da tamowa.  Horon na kwanaki 5 ya baiwa mahalarta damar samun Ilimi mai zurfi wanda yayi dai-dai da tsarin bada horo Hukumomi kula da tamowa ta Kasa, “in ji shi.
 Ya ce mahalarta taron sun fito ne daga ma’aikatar lafiya ta jiha da kuma guda biyar ADFIN da aka tallafa daga kananan hukumomin Bebeji, Dala, Kura, Tudun Wada, da Rimin-Gado da suka hada da jami’an tsaro (OICs), ma’aikatan lafiya na al’umma (CHEWs). Jami’an kula da abinci mai gina jiki, masu kula da lafiyar mata da yara (MCH), da Jami’an kula da Lafiya a matakin Farko (PHC).
 A wajen bude taron horaswar, manyan Masu bada Gudunmawa don ci gaban jihar Kano sun halarci taron tare da bayyana sakon su na fatan alheri ga Gidauniyar Aliko Dangote kan horar da
Jami’an IMAM.
 Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bude  taron horaswar wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Hajiya Amina A Musa.
 A jawabinsa na rufe taron, Kwamishinan ya yabawa kwazon Shugabannin Ma’aikatar kula da Lafiya a matakin Farko tare da ma’aikatansu Sakamakon juriyar da suke Yayin kwanaki 5 da akai ana basu horon.
 Daga nan sai ya yabawa gidauniyar bisa gudunmawar da take bayarwa wajen Gudanar da aiyukan Gina al’umma a Najeriya, da ma nahiyar Afrika baki daya, Sannan Kuma ya bayyana matukar jin dadinsa bisa ga dimbin gudunmawar da Alhaji Aliko Dangote yake bayarwa a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...