Ƴan Sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashin daji, Mai-ƴanmata a Zamfara

Date:

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji, Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-ƴanmata a jihar.

Rundunar ta ce Mai-ƴanmata, ɗan shekara 20 kacal da haihuwa, ya ƙware wajen garkuwa da mutane, fashin daji, satar shanu da sauran manyan laifuka a yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.

Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba N. Elkanah ne ya baiyana haka a taron manema labarai yayin da rundunar ta yi holon ɗan ta’addan a juya Laraba.

A cewar Kwamishinan, ” a ranar 28 ga Disamba da misalin ƙarfe 5 na yamma, yayin da su ke wani sintiri na sirri bayan sun samu bayanan sirri, sun cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-ƴanmata ɗan ƙauyen Mayasa a Ƙaramar Hukumar Zurmi.

Ya ƙara da cewa Mai-ƴanmata ya shiga komar ƴan sanadan ne lokacin yana shirin sanya shinge ya tsare bayin Allah domin ya yi garkuwa da su a daidai wani ƙauye mai suna Koliya.

Daily Nigerian ta rawaito Elkanah ya ƙara da cewa da a ɓangaren Turji Mai-ƴanmata ya ke, inda yanzu ya koma sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Kachalla Sani Black.

Ya ce an samu bindiga samfurin AK-47, sai kwanson harsashi 2, sai harsashi 3 da kuma babur guda 1.

Ya ce a na nan a na yi masa tambayoyi inda da ga nan za a ki shi kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Magance sheye-shaye ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Nugeria – Shugabar LESPADA

Daga Usman Usman   Ambassador Maryam Hassan shugabar kungiyar wayar da...

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...