Ku Taimaka Wajen Wayar da Kan Iyaye illar TikTok – Afakallah ya Fadawa ‘Yan Jaridu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar Tace Fina Finai da daf’i ta Jihar Kano ta jadda kudirin ta nayin aiki kafada-kafada da ‘yan Jaridu domin yaki da cin zarafin Al,umma .

KADAURA24 ta rawaito Shugaban Hukumar Malam Isma’ila NaAbba Afakallah ne ya bayyana hakan a lokacin daya Karfi bakuncin Shuwagabannin Kungiyar Masu gabatar da shirin al’amuran Yau da kullum a radio Wato Magazine programme dake Jihar Kano a Ofishin sa.

Malam Afakallah yace ‘yan Jarida Suna da Mahimmanci wajen temakon Al’umma tare da magance kalubalen da Ake fuskan ta musamman a Gidajen kallo.

Afakallah ya kara da cewa yanzu lokaci yayi da Gidajen Radio zasu temaka wajen wayar da kan Iyaye mata akan Wani abu TIKTOK,,, Wanda yake bata tarbiyya.

Kazalika Shugaban Hukumar tace Fina-Finan ya godewa Kungiyar Masu gabatar da shirin Magazine programme din bisa basu hadin kai da goyan bayan da Suke yi wajen aiki tare.

Da yake nasa Jawabin Shugaban Kungiyar Commared Sani Abdurrazak Darma yace sun kai ziyarar ne domin kulla alaka Mai Karfi da Hukumar tare da Yin aiki tare da Juna,,

Commared Sani Darma yace Kungiyar tana aiki ne domin hada kan masu gabatar da shirin Magazine da kuma yin aiki tare a Juna.

A karshen Shugaban Kungiyar Masu gabatar da shirin na Magazine din ya bukaci Hukumar ta cigaba da bawa ‘yan Jaridu gudunmawa domin kawo cigaban Al,umma.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...