Daga Zainab Muhd Darmanawa
Fadar shugaban kasa tayi allawada da Wasu labarai da suke cewa Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya na goyon bayan Wani bangare a Rikicin Jam’iyyar APC dake gudana a Jihar kano.
Kadaura24 ta rawaito Shugaba Buhari yace labarin ba gaskiya bane kuma shi baya Sanya baki a duk Wani al’amari da yake gaban Kotu.
Cikin Sanarwar da Babban Mataimakawa Shugaban kasa Kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya Sanyawa hannu yace labarin bashi da tushi ballantana makama,don haka ya bukuci al’umma su yi watsi da shi.
Ina Goyan bayan jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya ta, kuma ina so a sami hadin kai,amma ba na goyon bayan kowane bangare a Rikicin Jam’iyyar APC dake faruwa a Jihar kano.