Babban mai taimaka wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya kamu da cutar korona.
Duk da cewa bai samu amsa kiran da BBC ta yi masa ba, ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels, amma ya ce yana nan lafiya.
Ya ce bayan jin alamomin cutar ne ya killace kansa, kuma yanzu haka yana ci gaba da shan magunguna.
Kakakin shugaban wanda an yi masa rigakafin korona, ya tabbatar da cewa akwai kuma wasu ƙarin ma’aikatan fadar shugaban ƙasar da suma suka kamu a wannan lokaci.