Daga Zara Jamil Isa
Shugaban Kasa Muhd Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.
Kadaura24 ta rawaito Wani hadimin Shugaban kasa Mai suna Buhari Sallau shi ne ya Sanar da hakan tare da wallafa hotunna ganawar a Sahihin Shafin sa na Facebook.
Duk da har yanzu ba a bayyana abun da Suka tattauna ba,Amma ana ganin ganin nasu yana da nasaba da Rikicin da Jam’iyyar APC take fuskanta a Jihar kano.