Gwaggo ta Kaddamar da Musabakar Al-Qur’ani tsakanin Makarantun Firamaren dake Kano

Date:

Daga Safyan Dantala Jobawa
An yabawa uwar gidan gwamnan Kano, Farfesa Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje bisa kirkiro da shirin gasar wasanni tare da musabakar Alkur’ani maigirma ta yan makarantun firamare a jihar Kano.
KADAURA24 ta rawaito Sakataren ilimi na karamar hukumar Garun Malam, Alh Sani Mato ne, ya yi yabon a lokacin bude taron musabaka da gasar wasanni na makarantun Firamaren yankin wanda ya gudana a makarantar firamare ta Garun malam Kudu special.
 Ya ce bullo da irin wannan tsarin zai taimaka wajen zakulo dalibai masu basira da fasaha a makarantun firamare don kara samun cigaba a fannonin rayuwa.
Ya ja hankalin alkalan da za su jagoranci shirin, su kasance masu nuna gaskiya ba tare da nuna san-kai ko bangaranci ba.
 A nasa sakon, shugaban karamar hukumar ta Garun malam, Alh Mudansur Aliyu Dakasoye wanda  shugaban sashin kula da makarantun Alkur’ani da Islamiyyu na yankin, Comrade Ahmad Isah Garun malam ya wakilta, ya ce wannan abun alfahari ne kuma abun koyi ne ga sauran jahohin kasar nan, na irin bullo da musabakar Alkur’ani da gasar wasanni a makarantun wanda Hajiya Hafsat Ganduje ta yi, musamma ma a lokacin da dalibai ke zaune a gidan don gudanar da hutun karshen kowanne zangon karatu.
 Daga nan, shugaban karamar hukumar, ya sha alwashin duk dalibin da ya nuna kwazon shi tun daga matakin karamar hukuma da na shiyya har zuwa na matakin koli kuma ya sami nasara zai sami tagomashi mai girma. Sannan ya yi fatan alheri ga daliban da za fafata da su, da kuma godewa uwargidan gwamnar Kano bisa bullo da wannan tsari a fadin makarantun firamare na jahar Kano.
 Akalla Makarantun firamaren da suka sami damar shiga wannan gasar ta wasanin kwallon kafa da kwallon hannu da kuma kwallon tebur tare da yin musabakar Alkur’ani sun kai 17, wanda  suka  hadar da Garun mallam kudu special primary school da Garun mallam model primary school da Yadakwari Chedi primary school sai kuma Chiromawa Idi primary school da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...