Daga Zainab Muhd Darmanawa
Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Amince da nadin Manyan Ma’aikata da Wasu Yan Majalisar Zartarwar ta Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano Wato Kano Poly.
Cikin wata sanarwa da Jami’ar hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta Jihar Kano Halima Magaji Gwarzo ta aikowa Kadaura24 tace Gwamnan Ganduje ya Amince da nadin Mutanen ne Saboda kwarewar da sadaukar da Kai Wajen kula aiki da suke da shi yasa aka zabo su.
Waɗanda aka Nadan sun hada da :
1. Dr Muhammad Umar Kibiya – Deputy Rector.
2. Aminu Shu’aibu – Bursar.
3. Baffa Bello Bichi – Librarian.
4. Aliyu Muhammad Sani – Director, Academic Planning.
5. Dr Adamu Umar Alkali – Director, Works.
6. Dr Bello Adamu Dambatta – Director, Consultancy Services Unit.
7. Binta Abubakar Faruk –
Director, School of Management Studies.
8. Tijjani Yahaya Abubakar – Director, School of Environmental
Studies, Gwarzo.
9. Dr Muhammad Ahmad Sani – Director, School of Technology.
10. Dr Umar Muhammad Garzali – Director, School of General Studies.
11. Sulaiman Hashim Rano – Director School of Rural Technology and Entrepreneurship Development, Rano.
12. Kabiru Sharu Labaran – Director, Institute of Information Technology, Kura.
13. Zainab Abdulkadir –
Coordinator Program Visitation.
Sanarwar tace nadin ya bara aiki ne nan take,sannan ya bukace su, su tabbatar sun yi aiki kafada da kafada da duk Masu Ruwa da tsaki a Makarantar.