20 Disamba, 2021
Daga Zara Jamil Isa
Tsohon Gwamnan jihar Kano Sen. Engr. (Dr.) Rabiu Musa Kwankwaso ya yi rashin Dan uwansa Mai Suna Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso.
Kwamaret Inuwa Kwankwaso ya a safiyar yau Litinin 20 ga watan Disamba, 2021 a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya, ya rasu yana da Shekaru 64.
Marigayin tsahon ma’aikacin gwamnati ne da yayi ritaya kuma injiniyan noma da ya samu horo a Ibadan da Amurka wanda ya yi aikin Raya gandun daji a Kano Shekaru Masu yawa da suka gabata.
Cikin wata sanarwa da Jami’in tuntuba Cibiyar yada labaran Kwankwasiyya Sanusu Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 yace Kwamared Inuwa Kwankwaso ya bar matarsa, da ’ya’ya mata biyu Barr. Nafisa Inuwa da Zainab Inuwa da ‘yan uwa da dama.
Za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidan su da ke kauyen Kwankwaso a karamar hukumar Madobi a jihar Kano da misalin karfe 4:00 na yammacin yau.