Daga Rabi’u Sani Hassan
Babba Kotu Jahar Kano Mai Lambar 16 dake Miller road Karkashin Jagoranci Mai Sharia Jamilu Shehu Sulaiman ta bada Umarnin dakatar da Karamar hukumar Bichi daga rushe Kasuwar Bichi da tashin su zuwa lokaci da kotu zata saurare karar da wasu ‘yan kasuwa suka shigar gabatan ta.
KADAURA24 ta rawaito takardar karar mai dauke da sunayen Alh Haladu Bichi, Alh Umar Isa, Alh Zilyadani Bichi, Alh Sunusi Bako, Abdullahi Iliyasu, Abubakar Murtala da kuma Murtala Umar a Matsayin Wadanda su ka yi karar Karamar hukumar Bichi ta tare da Shugaban Karamar hukumar ta Bichi ta hannu Lauyansu Barrister A. I. Ma’aji a madadin Sauran yan Kasuwar ta Bichi.
Ta cikin takardar karar sun zargi Karamar hukumar Bichi da tashin su daga Kasuwar ba tare da wani gamsasshen bayani ba.
Sai dai a zaman kotun bisa jagorancin mai shari’a Jamilu Shehu Sulaiman kotun ta ba karamar hukumar umarnin dakatawa daga rushe Kasuwar ko tashin ‘yan kasuwar har sai ta saurarin Kara zuwa 2/2/2022.
Idan ba’a manta a satin da ya gabata ne aka fara rushe Kasuwar ta Bichi da nufin sauya Mata fasali zuwa na Zamani.