Sako Zuwa Yan Koren Manjo, Masu Fakewa A Inuwar Addini Da Shugabannin Arewa

Date:

Ra’ayin Muhammad Bashir Kano

Ba bu komai a cikin Haram sai ƙarya; kamar yadda ba bu komai a cikin Halal sai gaskiya! Ko muna so; ko muna ƙi; ko muyi magana akan tsaro; ko muƙi! Mun san matsalar nan mu ta shafa. Domin a yanayin da muke ciki, ba bu wata jiha a Arewa wanda ta tsira. Idan ba’a Kai hari a garin ku; to ana satar mutane. Idan ba’a satar mutane; to ana fama da matsalar daba, da kwace da tabarbarewar tarbiyya. Sabida haka, dole kowa sai tashi!

Shi lamari na yaƙi salo-salo ne da kuma rarrabuwar ayyuka. Wadansu su tafi filin-daga; wadansu su tsaya a bayan gari; wadansu kuma a bar su a cikin gari…wadansu ma labaran baiwa abokin gaba tsoro ne aikin su – kuma kowa da amfanin sa. Yanzu haka, a Arewacin Najeriya fa, yaƙi ne yake tunkarar mu, kuma tunda mutane suka ankara; suka fara magantuwa, wajibi ne aji koken su; ayi masu maganin abinda ya dame su. Ba magana ce ta wadansu daga cikin mu su riƙa fadin, “mu daga yau, ba za mu sake yin magana akan harkar tsaro ba…” to idan kun daina, sai me; sai kowa ma ya daina? Domin kuji, a ranar wadansu dubu za su fara – musamman wadanda aka kashe/sace na su.

Ita magana fa, furta ta zabi ne. kuma dama ai ba cewa akayi ‘lallai’ sai mutum ya yi magana akan tsaro ba! masu yin maganar ai akan rashin tsaro suke yi…kuma har idan abinda suke fada bai karya doka ba, to yaya kuke so ayi? Kuma na yi imanin cewa, kaso 90 cikin 100 na mutanen da suke da tsatstsauran ra’ayin yin shiru din nan, matsalar nan bata taba wani shaƙiƙinsu bane.

Maganar shirun nan, ai ba jiya aka fara kashe/sace mutane ba. A baya (masu yin maganar) anji muryoyinsu? Ba sai yanzu ba? Ko so akeyi ayi tayin shiru har sai kowa an tashe shi ya amsa tambayar “Man Rabbuka” Tukun? Sa’annan ku da kuke cewa masu yin magana sun raina Maluma, ku Malamai nawa kuka raina? Sau nawa ake ganin ku, kuna jifan su Dr. Ahmad Gumi, da Sheikh Nuru Khalid, da Malam Yabo da sauran su? Ko su ba Malamai bane? Ƙarya ne, basu san komai ba?

To yanzu, ga nan su Malam Musa Yusuf Asad ‘us-Sunnah, su Sheikh Al-Karmawy da sauran su; sun fara maganar – har Sheikh Asad ‘us-Sunnah yana cewa “duk Malamin da yayi shiru, al-halin yan ta’adda suna kashe mutane a mulkin nan; to Munafuki ne…” Amma, kalmar “DUK” da Malam Musa Yusuf Asad ‘us-Sunnah yayi amfani da ita, ‘DUK’ ce ta kowa? A’a, Malam yana magana ne da wadannan Malaman da aka gani a baya suna yin ‘campaign’ cewa a zabi gwamnatin nan.

Abin kaico, duk da wannan maganar sai ga shi wadansu mutane suna ta korafi, “ai gashi nan sabida jahilcin mutane, yanzu sai fadawa malamai magana suke…” sabida ai da kunya su fito fili; suce Malamai irin su Musa Asad ‘us-Sunnah basu san komai ba, yanzu bari su huce akan talakawa, sune marasa ilimi; kuma karkatacciyar Kuka mai dadin hawa.

Ƙarya ne, buhari bai sami goyon bayan ‘wadansu’ Malamai ba? Ko ƙarya akeyi masu cewa sunyi shiru? Ko ƙarya ne, da ake cewa irin wadannan malaman sun sauya halayen su – wadansu ma yanzu har gudun talakawa suke yi? Ai, a cikin mutanen da suke matsawa Malaman akwai masu kama suna, wadanda idan basu kama sunan Malami ba; suna kama sunan ƙungiya. Yaushe za kaga ana ambatar Malamai irin su Sheikh Dr Ahmad Ibrahim BUK, Dr Sani Rijiyar Lemu da sauran su?

Mutanen nan fa, dasu aka ribaci zukatan talakawa; akasa suka zabi gwamnatin Buhari har sau biyu sabida sun amince maku, shike nan idan lamari ya lalace, kuma suna so ayi gyara sai suƙi yin magana? Ku kuka nunawa talakawa Buhari sabida kun san shi, to yanzu da matsalar nan ta addabi kowa, wa kuke so a yiwa magana?

Sai anyi magana, sai suce “ai shirun da Malamai suka yi, shine yake nufin sun san ilimin zamantakewa dana sanin Allah…” hakane, amma a tarihin rayuwar Imam Malik, ai akwai lokacin da shugaban zamanin ya aike masa cewa yana jiran sa fada domin yaje; ya koya masa karatu. Imam Malik cewa yayi, a koma a fadawa Shugaban nan “shi ilimi zuwar masa ake yi; ba shine yake jewa mutum ba.”

Haka nan, lokacin Khilafar Haroon ‘ar-Rasheed a Baghdad, ai Imam Muhammad Ibn Idris ‘ash-Shafi’i lokacin da aka yi masa sharri, har takai ga an kawo shi cikin gidan Yari shi da daliban sa daga Makkah (bayan rasuwar Imam Malik da yan shekaru kadan), karshe Khalifa Haroon ‘ar-Rasheed ya fahimci cewa ƙarya akayi masa, ai ya nemi ya riƙa taimaka masa a sha’anin mulkinsa.

Kuma, kasancewar a lokacin matsalar Mu’utazilat ta fara naso, dayin dauki dai-dai a cikin daliban ilimi, Imamu ‘ash-Shafi’i ai da kan sa yake baiwa Khalifa Haroon ‘ar-Rasheed shawarwari akan hadarin su. Lokacin duk su Imam Ahmad Ibn Hambal suna matakin manyan daliban ilimi…amma ko lokacin da Imam Ahmad Ibn Hambal ya bunƙasa, kuma matsalar Mu’utazilawa ta fadada – bayar rasuwar Haroon ‘ar-Rasheed, har ta kai Khalifan daya gaje shi ya sa a gayyaci Imam Ahmad Ibn Hambal da sauran Malaman Birnin Baghdad domin su amsa tambaya akan cewa Al-Qur’ani Maganar Allah Ce; Ko Kuma Halittar Allah? Ai da yawa fitowa suka yi; suka ce Al-Qur’ani Maganar Allah Ne, kuma a gaban Khalifan.

Ga wadanda za suce “ai wannan matsalar, magana ce ta Al-Qur’ani” su sani cewa wannan kuma itama magana ce ta zubar da jini…kuma Allah Yana ganin girman ta! Kuma tsayar da zubar da jinin mutane hakki ne akan shugabanni da kuma kowa. Kuma sabida Annabi Muhammad Sallallahu Alayhi Wasallam Ya sani cewa a lamari na zamantakewa akwai matakai da yawa wadanda dai-daikun mutane ba za su iya dauka ba, sai shugabanni – shine yasa Yayi umurni da idan mun ga ana aikata laifi; mu kawar da hannayen mu, idan ba za mu iya ba; mu kawar da harasan mu, idan ba za mu iya ba; mu ƙyamace shi – wanda shine mafi ƙarancin imani.

Ƙarfin yaƙar yan ta’addar nan lallai sai gwamnati, sune za su iya kawar da su da hannayen su, na ba ki kuwa gwamnati da al’uma sunyi tarayya a ciki – sabida haka a bar mutane suyi magana, tunda wadanda ake kira da suyi, ana zargin ba yi suke yi ba!

A wannan gaba, dole ne mu yarda cewa duk da akwai sakaci da kuma rashin bibiyar yadda ake haƙiƙanin yaƙar yan ta’addar nan daga bangaren gwamnatin Najeriya, ba za kore duk hobbasa din take yi ba. Sabida wataƙila da ba sa yin ƙoƙari ko yaya, da ƙasar bata zaunu ba, da wataƙila mu masu yin maganar ma, sai dai mu riƙa yi daga wadansu ƙasashen da muke tsere domin gudun hijira.

Kiran duk da ake tayi dama bai wuce a ƙara zage damtse ba; a cigaba da ƙoƙari, sabida alƙawarin da aka daukarwa mutane ke nan – wanda rashin cika shi, zubar da mutuncin duk zuri’a ne. Domin yanzu, na tabbatar da cewa duk Wani abu daya shafi Buhari ba mai mutunci ne a idanun mafi yawan talakawan ƙasar nan ba, koda yake akwai wadanda ba su da dalili.

Kuma, ba za mu taba mantawa da rashin kishin da wadansu daga cikin sauran shugabannin Arewa ba, kamar Gwamnonin Arewa, da Sanatoci, da Yan Majalisun Wakilai, da duk wani shugaba zababbe ko na nadi – wanda suke nuna mana ba. Al’umar Arewa ‘sam’ ba muyi sa’ar shugabanni ba, kuma wajibi ne mu taru; mu sauya su. Mutane ne, wadanda suka sarayar tare da sayar da yancin mu. Ba bu abinda suke yi sai bukuwa a lokutan da muke cikin alhini; suke dariya a lokutan da muke tsaka da yin kuka. Wadannan ba shugabanni bane!

Sai batun zargi/tabbacin cewa akwai sa hannun ƙasashen ƙetare a lamarin nan, wanda ko a kwanan baya an kama wata ƙungiya da laifin baiwa wadansu matasa a jihar Borno horon harbi a wani otal, amma tunda aka saki labarin dakatar dasu, bamu sake jin labarin yadda akayi da matasan ba; bamu ji ance a shigar da ƙara ba, ko wani matakin mai da aka dauka akan ƙungiyar ba. Najeriyar nan fa kasar mu ce, ba dai-dai bane mu zuba idanu, wadansu mutane daga wadansu ƙasashen suna cutar damu ba, sabida sun gano wani arziƙi da muke su ba.

Allah Ya taimakawa shugabannin mu, su dawo kan hanyar mai kyau; suyi abinda ya dace. Allah Ya ba mu zama lafiya da yalwar arziƙi.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...