Habbaka Ilimi: Masana sun baje kolin ilimi da dabarun rubuta kundin bincike a karamar hukumar D/Tofa

Date:

Musa Mudi Dawakin Tofa.
Kungiyar Malaman Makarantun Gaba da Sakandire ‘Yan Asalin Karamar Hukumar Dawakin Tofa wato Dawakin Tofa Academic Forum DAF ta jagorancin gudanar da taron bita ta yini guda wadda aka gudanar a dakin taro na Makarantar Sakandiren Maza  dake cikin garin Dawakin Tofa a jihar Kano.
KADAURA24 ta rawaito yayin da yake bayyana makasudin shirya taron bitar Ma’ajin Kungiyar Malam Junaidu Danladi ya ce sun Shirya bitar ne da nufin ba da tasu gudunmawar wajen inganta harkokin Ilimin kannensu da ‘ya’yansu da ke yankin.
Yace wajibi ne a garesu su rika shirya irin Wannan bitar wadda yace sun yi Imani zata taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin Ilimi,tare kuma ba bar yan baya Wani abun alkhairi Wanda za’a dade ana mora.
Kasancewar Kungiyarmu ta masana ce, Kuma bincike na daya daga cikin ayyukanmu a wuraren aikin kuma mafi yawancinmu na ci gaba karo karatu musamamma digiri na biyu dana uku shi yasa Muka ga dacewar mu yi amfani da manyan masana da gogaggun cikinmu don mu  kara koyar hanyoyi da dabarun bincike”. Inji shi 
 Yace sun shirya musu bitar ne domin su kara samun wayewa da koyan dabarun rubuta kundin bincike a fannonin ilimi da dama.
Malam Junaidu Danladi yace an  gayyaci mahallarta bitar ne daga kananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa kuma sun amsa kira.
A yayin bitar masana hudu ne suka gabatar da makaloli akan batutuwa daban-daban: Dokta Tijjani Sabi’u Imam daga Jami’ar Bayero dake Kano ya  gabatar da makala akan “Kurakurai da ka’idojin da mai rubuta kundin bincike zai kiyaye”, sau Farfesa Muhammad Nasir Yaro daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse ya gabatar da takarda mai taken “Gabatarwa da bincike a matakin farko” ,yayin da takarda ta uku Dokta Nura Yaro Dawakin Tofa daga Jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Kano ya gabatar akan “Siyasar  mu’amullantar masanin dake duba mai yin bincike” da kuma Malam Salmanu Ado daga Kwalejin Ilimi da Share Fagen Shiga Jami’a dake Kano da ya gabatar da takarda ta karshe akan  “Hanyoyin yin bincike a fannoni dabam-dabam”.
Malama Muhammad Hadi Ahamd daga Kwalejin koyon kiwon lafiya ta jihar Kano kuma guda daga cikin ‘ya’yan kungiyar DAF da Ahmad Sani Ibrahim daga cikin al’ummar gari da suka hallarci taron bitar, a madadin mahallartan su bayyana farin cikinsu, sannan suka ce sun samu alfano mai tarin yawa a yayin gabatar da bitar da kwararrun kuma gogaggun masanan suka gabatar musu”.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...