Gwamnatin Kano ta yabawa UNICEF Saboda ba da tallafi a fannin Lafiya

Date:

Daga Zara Jamil Isa
An bayyana rigakafin kamuwa da cututtuka a tsakanin mutane a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ta sanya a jihar Kano.
 Hakan na tabbatuwa ne ta hanyar aiwatar da manufofin Gwamnatin Jihar Kano karkashin Jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje a fannin kiwon Lafiyar al’umma.
 Kwamishinan Lafiya na Jihar kano  Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa me ya bayyana hakan yayin da ya wakilci gwamna Abdullahi Umar Ganduje a wajen bikin raba kayayyakin kariya da tsaftar muhalli ga ma’aikatar da hukumominta da cibiyoyin kiwon lafiya wanda ya gudana jiya a  Hukumar Kula da Lafiyar  Magunguna da Abun Ciki (DMCSA).
Cikin Wata sanarwa da Jami’ar hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Lafiya Hadiza M Namadi ta aikowa Kadaura24 tace Dokta Tsanyawa ya bayyana cewa UNICEF ta bayar da tallafin ne ga gwamnatin jihar domin tabbatar da tsafta a cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar a matsayin babbar hanya ta hana yaduwar kwayoyin cuta da cututtuka a fadin jihar.
 Yayin da yake bayanin cewa a duniya an amince da tsaftar muhalli a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da ake bukata na rigakafin cututtuka, ya yabawa kokarin UNICEF na ba da gudummawar kayayyakin ga jihar.
 A nasa jawabin babban daraktan hukumar samar da magunguna ta Jihar Kano Pharmacist Hisham Imamudeen Shima ya yaba wa UNICEF a matsayin babbar abokiyar ci gaba wanda burin su shi ne bunkasa harkokin kiwon lafiya a kasar nan dama duniya baki daya.
 Pharmacist Hisham ya bukaci cibiyoyin lafiya da su yi amfani da kayan da aka ba su cikin adalci.
 A nasa bangaren, Wakilin UNICEF ya ce kayayyakin da aka bayar sun hada da kwandon shara, Google ido, abin rufe fuska, Sinadarin  wanke hannu, wanke ruwa, chlorine, riguna, bokiti da mopper.
 Ya ce UNICEF tana ba da tallafi a sassa daban-daban na kiwon lafiya inda ya kara da cewa za su ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar Kano Wajen yaki da  COVID-19.

2 COMMENTS

  1. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...