Tsagin Yari a jam’iyyar APC ta Zamfara sun ce zasu daukaka Karar hukuncin Rushe Shugabanin jam’iyyar

Date:

Daga Abdulrazak B Kaura

Tsagin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar Shattiman Zamfara a jam’iyyar APC yace ta kowacce fuska ba zai lamunci hukuncin da Wata Babbar kotun tarayya dake gusau ta yanke ba, Wanda ta kori karar da Suka shigar Su na Kalubalentar rushe shugabanin jam’iyyar da kwamitin rikon uwar jam’iyyar yayi .

Da yake tsokaci Kan hukuncin kotun, Shugaban jam’iyyar APCn tsagin Abdulaziz Yari Wato Hon. Lawan M Liman Gabdan kaura yace zasu daukaka Kara har Zuwa kotun koli domin tabbatar da an yi musu adalci.

Hon. Lawan M Liman yace dama basu yi mamakin hukuncin kotun ba, Saboda tuni a ganawar da yayi da Manema labarai Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya bayyana yadda Hukuncin zai kasance, Amma yace hakan ba zai sanyaya musu gwiwa ba wajen daukaka karar don tabbatar da an yi musu adalci.

Cikin Wata sanarwa da Sakataren yada labaran tsagin Abdulaziz Yari  Hon. Ibrahim Muhammad (Dan madamin Birnin Magaji) ya Sanyawa Hannu Kuma aka aikowa Kadaura24, yace in har kotun koli zata yanke hukuncin da yasa jam’iyyar APC ta rasa kujerunta a Zaben Shekara ta 2019 , to Yanzu ma Suna da kwarin gwiwar Samun nasara a kotun gaba.

Ya yabawa kokarin jagoransu tsohon Gwamnan Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar bisa tsayyayarsa wajen jagoranci da kuma masu Ruwa da tsakin tsagin tun daga matakin Jiha Kananan Hukumomi da Kuma Mazabu a kafatanin Jihar Zamfara Saboda irin Gudunmawar da suke bayarwa a Koda yaushe ,Kuma yace su na da kyakykyawan zaton Allah zai basu nasara a Wannan gwagwarmayar da suke.

3 COMMENTS

  1. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי

  2. קמגרה הוא אחד מתחליפי הויאגרה הנפוצים והאיכותיים ביותר, אשר נמכר בעשרות מיליוני יחידות בכל רחבי העולם. מדובר בתכשיר המטפל בבעיות השגת זקפה אשר מקורן בגורמים שונים, וזאת על ידי הרחבת כלי הדם ובעיקר באזורים הקשורים ליחסי המין. ההרחבה מאפשרת זרימת דם משופרת לאיבר המין, ומכאן להשגת זקפה מלאה וממושכת יותר. fabric token uniswap liquidity pool

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...