Daga Shekara ta 2022 Shan Shisha a Kano Laifi ne – Ganduje

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin dakile shan Shisha a jihar Kano.

Manajan Daraktan hukumar yawon bude ido ta jiha Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa ya bayyana haka a wata hira da yayi da Daily News 24.

Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa ya ce hakan wani mataki ne da gwamnati za ta dauka na kara tsarkake jihar Kano daga munanan ayyuka da laifuka da ka iya barazana ga tarbiyyar matasa.

Lajawa ya kara da cewa tun ranar 3 ga watan Nuwamba, Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar, wadda za ta fara aiki a shekarar 2022.

Dokar ta hada da masu wuraren gudanar da bukukuwa, da kuma dakunan yara ‘yan kasa da shekaru 18 a cikin otal a fadin jihar.

Dokar ba ta tsaya nan ba, ta hada da duk dillalan da ke sayar da shisha, da masu siyar da shi ko masu sana’anta.

Tuni hukumar mu ta dauki matakin jagorantar masu wadannan sana’o’in, domin ganin cewa ba su karya wannan doka da za ta fara aiki nan ba da dadewa ba,” Yusuf Ibrahim Lajawa.

Manajan daraktan ya kuma ce ya zama wajibi al’ummar jihar Kano su baiwa hukumar kwarin gwiwar samun nasara a ayyukan ta.

14 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...