Daga Tijjani Mu’azu Aujara
Allah ya yiwa tsohon Hakimin karamar hukumar Dambatta, kuma kwamishinan ilimi na farko a jihar Kano Alhaji Mukhtar Adnan rasuwa.
Daya daga cikin ‘ya’yansa Baba Ado ne ya tabbatar wa da BBC labarin rasuwar tasa.
Ya ce ya rasu ne dab da asubahin ranar Juma’a a sibitin UMC Zahir da ke unguwar Jan Bulo inda ya yi jinya
Marigayi Alhaji Mukhtar Adnan ya zama dan majalisar sarki mai nadin sarki tun a shekarar 1954, inda bayan shekaru 9 da samun wannan mukamin a fadar Sarkin Kano ne, suka nada marigayi Dr. Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a shekara ta 1963.
Daily News24 ta rawaito Marigayi Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan shi ne kwamishinan Ilmi na farko tun a tsohuwar jihar Kano, haka zalika ya taba rike bulaliyar majalisar tarayyar Najeriya.
A lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ne aka sanya sunan marigayin a Kwalejin Kimiyya ta maza dake kan titin State Road wato ‘Day Science‘.