Na kadu Matuka Dana Sami Labarin Hadarin Jirgin Ruwa a Bagwai – Alhassan Ado

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar wakilai ta Kasa Kuma Dan Majalisar dake wakiltar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada Hon. Alhassan Ado Doguwa ya Mika Sakon ta’aziyya da jajantawa ga al’ummar Jihar Kano bisa Iftila’in hatsarin jirgin Ruwa (kwale-kwale) a Garin Bagwai.

Sakon ta’aziyyar na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar wakilai Auwal Ali Sufi ya sanyawa hannu Kuma aka aikowa Kadaura24.

Sanarwar ta ce Shugaban Masu Rinjaye Wanda shi ne Sardaunan Rano ya kadu sosai Lokacin da ya Sami labarin hadarin Wanda yayi sanadiyyar Rasuwar Ɗalibai kusan 27 da Kuma Waɗanda Suka jikkata.

 

Tallafi :Alhassan Ado ya raba Naira Miliyan 70 ga al’ummar Tudun Wada da Doguwa

Wannan Lamari al’amari ne daga Allah Wanda Babu wanda ya Isa ya Hana faruwar sa, Amma dai lamarin bai yi mana dadi ba, muna addu’ar Allah ya gafartawa Waɗanda Suka rasu, Waɗanda Suka jikkata Kuma Muna fatan Allah ya basu Lafiya”. Inji Hon. Doguwa

Hon. Doguwa ya Mika Sakon ta’aziyya da jajantawa ga Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da al’ummar Karamar Hukumar Bagwai dama na Jihar kano baki daya.

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi fatan Allah ya baiyana Waɗanda Suka nutse a Cikin Ruwan, Sannan yayi fatan Allah ya Kare afwar hakan anan gab.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...