Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Alhaji Hassan Garban kauye farawa ya Mika Sakon ta’aziyya ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo bisa rasuwar kanwar Mahaifinsa Hajiya Hadiza Galadima Abubakar.
Cikin Wata sanarwa dauke dasa Hannun Mai taimakamsa Kan harkokin yada labarai Shazali farawa ya aikowa Kadaura24 yace Rashin Hajiya Hadizan Babban rashi ne ga al’ummar Jihar Kano Baki Daya.
Shugaban Karamar Hukumar ta Kumbotso ya bayyana cewa “Don haka ina mika wannan ta’aziyya ga kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo, da daukacin iyalanta, da al’ummar garin Garo da karamar hukumar Kabo, a madadin al’ummar Karamar Hukumar Kumbotso.
Shugaban Wanda yanzu gaka ke kasar Saudiya Domin Sauke fararin Umara ya Kuma yi addu’ar Allah ya gafarta Mata, Sannan ya bukaci ‘yan uwa da su Kara Hakurin rashinta.