Rikicin APC : Ranar Litinin Za’a Fara Sulhunta Bangaren Ganduje da Shekarau

Date:

Daga Nura Garba Jibril
Kwamitin sulhun jam’iyyar APC ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin yin adalci ga fusatattun ‘yan jam’iyyar da Suka gabatar da korafin su ga Uwar jam’iyyar domin samun zaman lafiya mai dorewa a Jam’iyyar.
 Shugaban kwamitin Sanata Abdullahi Adamu kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne ya bada wannan tabbacin a wata ‘yar gajeriyar hira da manema labarai a Abuja.
 Sanata Abdullahi ya ce manufar ita ce a tabbatar da an sulhunta duk wadanda suka samu sabani  kafin babban taron jam’iyyar na kasa ya zo nan ba da dadewa ba.
 Shugaban Kwamitin ya kara da cewa, shugabannin jam’iyyar sun damu matuka da Matsalolin da Suka dabai baye Jam’iyyar Musamman a matakan jihohi, Inda ya bada tabbacin zasu Samar da zaman lafiya tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar ta kowane hali.
 Sanata Abdullahi Adamu ya ce kwamitin ya yanke shawarar fara aikinsa a jihar Kano a Ranar litinin din nan domin warwaren Matsalar da jam’iyyar APC ta fuskanta don ya Zama masomin Nasarar Kwamitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...

Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce...

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...