Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar koli kan harakokin tsaro a fadarsa a Abuja inda ake sa ran za a sanar da shi halin da ake ciki game da tsaro a ƙasar.
Taron ya ƙunshi mataimakinsa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadarsa Chief Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro Manjo General Babagana Monguno da kuma babban hafsan sojin Najeriya Janar Leo Irabor.
BBC Hausa ta rawaito a wajen taron ne Shugaban ya ƙara wa babban dogarinsa Laftanar Kanal YM Dodo girma zuwa matsayin Kanal.