Rashin Ruwa a Kano: Gwamnatocin baya ne Sila – Ganduje

Date:

  • Daga Sadiya Muhammad
 Gwamnatin jihar Kano ta ce ta dauki kwararan matakai na magance matsalar karancin ruwan sha a jihar Kano Baki daya.
 Kwamishinan albarkatun ruwa Alhaji Sadiq Aminu Wali ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
 Ya ce kalubalen karancin ruwan sha da ake fama da shi a wasu yankunan jihar matsala ce da ake danganta ta da al’amura da dama da aka gada daga gwamnatocin da suka gabata a Kano.
 Alhaji Sadiq Aminu Wali ya bayyana cewa daya daga cikin manya-manyan dalilan da suka haifar da karancin ruwa a Kano sun hada da yawan Al’umma, lalacewar bututun da aka gada daga gwamnatocin baya, da kuma amfani da na’urorin da ba su da inganci  daga cikin kamfanonin sarrafa ruwa da dai sauransu.
 “Tun zuwan gwamnatin jihar Kano ta dauki matakan shawo kan wannan kalubale, mun gana da hukumomin bayar da tallafi da kuma wata Hukuma daga Kasar Faransa don gyaran manyan cibiyoyin ruwa guda biyu a cikin birnin Kano na Challawa da Tamburawa” inji Wali
 Ya ce gyaran da za a gudanar a manyan madatsun ruwa guda biyu sun hada da gyaran kayiyyaki Aiki tunkudo ruwa, bututu, da mitoci, da fadada wasu Kananan madatsun a kananan hukumomin jihar.
 Kwamishinan ya kara da cewa, idan aka kammala gyara matsalar karancin ruwa za ta zama tarihin a Kano.
 Alhaji Sadiq Aminu Wali ya danganta wasu daga cikin manya-manyan abubuwan da ke haifar da karancin ruwa da rashin isashshiyar wutar lantarki, yana mai jaddada cewa idan babu isasshiyar wutar lantarki akai-akai famfunan ruwa ba za su iya fitar da ruwan ta cikin bututun ga jama’a yadda ya kamata ba.
 “Domin magance wannan matsalar a kwanakin baya gwamnatin jihar Kano ta kulla yarjejeniya da kamfanin samar da wutar lantarki na Neja Delta domin samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba a Kamfanoninmu, amma idan muka fadi gaskiya muna fuskantar kalubale da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano Kedco wanda ya mallaki wutar lantarkin, sun ki amincewa da yarjejeniyar domin kedco ce take raba Wutar lantarki a Wannan  yankin, Amma muna kokarin magance matsalar.
 Alhaji Sadiq Aminu Wali ya bukaci jama’a da su cigaba da bayar da gudunmawarsu a can wajen kula da ayyukan ruwa da kayan aiki a yankunan su da nufin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...