Daga Nura Abubakar
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta kashe gobarar da ta kone ofisoshi guda biyar, a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano dake Wudil (KUST) a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Alhaji Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai ranar Lahadi a Kano.
“Mun samu kira a sashin mu na Wudil daga jami’an tsaro da misalin karfe 12:04 na safe cewa gobara ta tashi a wani benen Jami’ar.
Bayan samun labarin, mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 12:07 na safe, domin shawo kan lamarin,” in ji sanarwar.
Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta kone dukkan ofisoshin guda biyar gaba daya.
Ya kara da cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
Ya bukaci jama’a da su kara yin taka-tsan-tsan da kuma daukar matakan kariya domin gudun tashin gobara Musamman a Wannan Lokaci da sanyi yake kara kamari.